Espania Ta Soke Cinikin Makamai Na EUR Miliyon 700 Da HKI Saboda Kissan Kiyashi A Gaza

Gwamnatin kasar Spaine ta soke kontaragin sayan  makama daga HKI wadanda yawansu ya kai Euro Miliyon 700, saboda kissan kiyashin da ke faruwa a gaza.

Gwamnatin kasar Spaine ta soke kontaragin sayan  makama daga HKI wadanda yawansu ya kai Euro Miliyon 700, saboda kissan kiyashin da ke faruwa a gaza.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa a jiya Litinin ne gwamnatin firay minister Pedro Sanchez  ta bada wannan sanarwan ta kuma kara da cewa makaman su ne makamai masucilla rokoki samfurin Elbit kirar HKI.

Labarin ya kara da cewa Madrid ta soke wani kontaragi wanda ya kai Eur miliyon 287 da HKI. Na sayan garkuwan tankunan yaki wadanda za’a kerasu a kasar karkashin lacicin HKI a kasar Espania.

Banda haka firay minister Pedro Sanchez ya bukaci a haramta HKI daga dukkanin wasannin nakasa da kasa saboda kissan kiyashin da take aikata a gaza a ranar Lahadin da ta gabata.

Gwamnatin kasar ta Espania tabayyana cewa tanada shirin daukar wasu karin matakan kan HKI saboda kissan kiyashin datake aikatawa Gaza.

Daga cikinsu har da haramtawa dukkan yahudawan da suke da hannu cikin kissan kiyashin shiga kasar Espania .

Sannan akwai takunkuman tattalin arzikin na hana sayan dukkan kayakin da ake kerawa a kasar Falasdinu da aka mamaye.

Daga karshen gwamnatin kasar Espania ta zargi kasashen turai kan nuna fuska biyu a kissan kiyashin Gaza, idan an kwatanta da na Ukraine.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments