Ministan tsaro na kasar Venezuela Vladimir Padrino López ya gargadi gwamnatin Amurka dangane da duk wani kokari na kaiwa kasar Venuzuela hare hare saboda kifar da gwamnatin shugaba Nicolas Madoro. Tare da fakewa da fasakorin kwayoyi.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Vladimir yana cewa take-taken gwamnatin Amurka na sojojin da ta kawo a teken carebian ya yi kama da takalar yaki ne da kasar Venezuela , kuma idan haka ne, to sojojin sa a shirye suke su fuskance su, su kumakare kasarsu.
Kamfanin dillancin labaran IP nakasar Iran ya bayyana cewa, Amurka ta fara kai ruwa rana da gwamnatin shugaba Madoro ne tun lokacinda shugaban Amurka Donal Trump ya bayyana shugaban kasar ta Venezuela a matsayin dan kwaya kuma mai fasa korin kwayoyi.
A halin yanzu dai gwamnatin Trump ta tura sojojinta zuwa tekun Carabian kusa da kasar ta Venezuela da nufin kifar da gwamnatin Nicolas Madoro.