An fara taron hukumar IAEA ta kasa da kashe karo na 69TH a jiya Litinin, a birnin Vienna inda a taron ne ake fayyana al-amura masu muhimmanci da suka shafi makamashin Nukliya a duniya, kuma tuni shugaban hukumar makamashin Nukliya ta kasar Iran Muhammad Eslami yake jagorantar tawagar Iran a taron.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran, ya bayyana cewa a irin wannan taron na shekara-shekara inda kuma aka tattauna abubuwa masu muhimmanci dangane da makamashin Nukliya.
Kafin ya bar nan Tehran Eslami ya ce zai gabatar da al-amura wadanda suka shafi sabawa dokokin hukumar da IAEA ta kasa. Ya kuma kara da cewa JMI ba zata saba barin hakkinta tashe makamashin Uranium wanda ya zo cikin yarjeniyar NPT.
Eslami ya kammala da cewa wannan taron wuri ne na bayyana sabbin ra’a yi da kuma damuwar da kasashen duniya suke fauskanta da ya shafi makamashion nukliya.
Daga karshe shugaban hukumar makamashin nukliyata kasar Iran ya ce,Iran zata gabatar da korafi kan hare-haren HKI da Amurka kan cibiyoyin makamacin Nukliya na kasar Iran, amma kumahukumar ta kasa yin allawadai da hare-haren.