JMI ta zama zakara a gasar damben girgajiya ta kasa da kasa bayan ta fara shiga gasar shekaru 12 da suka gabata .
Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi yana taya tawagar yan damben murna da nasarar da suka samu, ya kumakara da cewa wannan shi ne nasara ta wasannan kasa-da kasa har guda 6 wadanda Iran take samun lambobin zakara a cikinsu a wannan shekarar.
Labarin ya kara da cewa yan damben Iran sun sami wannan nasarar kwana guda kafin a kammala gasar.
An bayyana nasarar da yan damben Iran suka samu ne a jiya Litinin da yamma a birnin Zagreb inda aka gudanar da gasar. Sun sami lambobin yaboguda 5 a gasar wanda ya basu damar lashe gasar.
Labarin ya kara da cewa tawagar yan damben Iran sun shiga gasar ne shekaru 12 da suka gabata, kuma Amir Hussain Zare ya fita da lambar zinari a dambe mai nauyin kilogram 125.
Bayan ya sami nasara a kan dan wasan Amurka. Ahmad Mohammadnejad-Javan ya tashi da Azurfa daya sannan Kamran Ghasempour mai nauyin (86kg), da Amirhossein Firoozpour mai nauyin (92kg). da kuma Mohammad Nahodi duk sun tashi da tagulla 3.