Baqa’i: Kowace Kasa A Duniya Tana Da Hakkin Mallakar Makamashin Nukiliya Na Zaman Lafiya

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya tabbatar da haƙƙin kasashe na haɓakawa da amfani da makamashin nukiliya na zaman lafiya Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Jamhuriyar

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya tabbatar da haƙƙin kasashe na haɓakawa da amfani da makamashin nukiliya na zaman lafiya

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran, Isma’il Baqa’i, ya yi ishara da shawarar da Iran ta gabatar na daftarin kudurin da ya haramta kai hare-hare kan cibiyoyin makamashin nukiliyar kasashe masu zaman lafiya, yana mai cewa: Dukkanin kasashe na da hakkin yin amfani da makamashin nukiliya don zaman lafiya da kuma hakkin samun ingantacciyar kariya daga duk wani hari ko barazanar kai hari.

A cikin sakon da ya aike ta dandalin X a yau Talata, Ismail Baqa’i ya yi ishara da shirin Iran a babban taron hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa (IAEA) da ake yi yanzu a Vienna, don ba da shawarar daftarin kudurin da ya haramta kai hari kan cibiyoyin makamashin nukiliyar kasashe masu zaman lafiya. Ya ce: “Iran, tare da China, Nicaragua, Rasha, Venezuela, da Belarus, sun gabatar da wani daftarin kuduri ga babban taron hukumar IAEA kan haramta kai hare-hare da kuma barazanar kai hare-hare kan cibiyoyin makamashin nukiliya da ke karkashin hukumar sa-idon ta IAEA bisa tsarin kare martabar yarjejeniyar hana yaduwar makaman nukiliya.”

Ya kara da cewa: “Kamar yadda aka bayyana a cikin daftarin kudurin, dukkan kasashe na da ‘yancin yin amfani da makamashin nukiliya domin zaman lafiya da kuma ‘yancin samun ingantacciyar kariya daga duk wani hari ko barazanar kai hari.”

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments