Jaragen yaki wadanda ake sarrafasu daga nesa wato Drones sun fada kan wurare masu muhimmanci a kudancin kasar Falasdinu da aka mamaye, yan sa’o’in da suka gabata.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto kakakin sojojin kasar Yemen Burgediya Janar Yahyah Saree yana fadar haka a dazo-dazon nan .Ya kumakara da cewa. hare-haren sun hada da Drons guda 4, 3 daga cikinsu sun fada kan tashar jiragen sama na Ramon da ke kusa da Ummu Rash-rash ko Ilat kamar yaddayahudawan suke kiransa. Sannan guda kumaya fada kan sansanin sojojin HKI na Negev duk a kudancin kasar.
Ya ce an kai hare-haren ne don goyon bayan Falasdinawa wadanda HKI take kashewa tunkimani shekaru biyu da suka gabata. Sannan sanarwan ta kara da cewa hare-haren zasucigaba matukar an ci gaba da yaki a Gaza.
Ya zuwa yanzudai sojojinyahudawan sun kashe Falasdinawa kimani 65,000. Tun daga cikin watan octonan shekara ta 2023.