Shugaban Iran Yace Makiya Suna Son gwara Kan Musulmi Don Sace Arzikinsu

Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkiyan ya bayyana cewa makiya suna son cusa gaba a tsakanin kasashen musulmi don su sami damar sace arzikin makamashin da

Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkiyan ya bayyana cewa makiya suna son cusa gaba a tsakanin kasashen musulmi don su sami damar sace arzikin makamashin da sunke da shi da kuma jawo hankalin kwararrun da kasashen musulmi suke da shi don amfanin kansu.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalyo shugaban kasar yana fadar haka a safiyar yau Alhamis, a birnin Ardabil da ke kusa da ke iyaka da kasar Azarbaijan daga arewacin kasar.

Masoud Pezeshkian ya je landin ne don kaddamar da ayyukan ci gaban kasa da ayyukan raya kasa wadanda aka kammala a yankin har guda 72.

Shugaban ya kara da cewa, da wadannan kasashe basu da kome ba zasu zo su nemi wani Abu a wajemmu ba. Don haka suna neman arzikimmu ne da kuma kwararrummu. Ana saran shugaban zai gabatar da jawabi da dama a cikin rangadin da yake yi a lardin Ardabil na arewacin kasar ta Iran.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments