Asusun “UNICEF” Ya Yi Gargadi Kan Bala’in Jin Kai A Gaza

Asusun Kula da Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya ya yi gargadi karuwar bala’i na jin kai a Gaza Kazem Abu Khalaf, kakakin hukumar UNICEF

Asusun Kula da Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya ya yi gargadi karuwar bala’i na jin kai a Gaza

Kazem Abu Khalaf, kakakin hukumar UNICEF a Falasdinu, ya tabbatar da cewa: Abin da ke faruwa a Gaza ba a taba ganin irinsa ba, yana mai cewa har yanzu yana ci gaba da tuntubar wasu ma’aikatan jin kai da dama da suka yi balaguro zuwa yankunan da ake fama da rikici, da bala’o’i, da wuraren yaki a duniya, kuma dukkansu, ba tare da togiya ba, sun amince cewa, ba su taba ganin wani yanayi mai kama da abin da ke faruwa a Gaza ba.

Abu Khalaf ya yi nuni da cewa: Mutanen yankin Zirin Gaza sun fara fama da yunwa, sannan kuma kishirwa, gami da fuskantar kisa, yayin da aka jibge kayan agajin jin kai a kan iyakar da ke da tazarar kilomita goma kacal. Motar bas guda na iya daukar sa’a guda-ko kuma akalla sa’a daya da rabi kafin ta isa tsakiyar zirin Gaza da agaji, amma sojojin mamayar Isra’ila ba za su kyale ta.

Ya bayyana cewa, kasashen duniya suna nuna halin ko-in-kula, tare da nuna rashin damuwa da daukan abin da muhimmanci daga Larabawa a hukumance da kuma juya baya daga al’ummar Larabawan.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted