Hukumomin rikon kwaryar Siriya sun rufe hanyoyin zuwa birnin Sweida bayan sake bullar wani tashin hankali
Dakarun gwamnatin Siriya na ci gaba da rufe hanyoyin da ke shiga lardin Sweida da ke kudancin kasar tun daga wayewar garin ranar Asabar, bayan kazamin fadan da aka gwabza tsakanin kabilar Bedouin da mayakan Duruz a cikin birnin. A halin da ake ciki, ana ci gaba da kokarin da ake yi na cikin gida da waje na wanzar da tsagaita bude wuta da kare fararen hula.
Ana zaman dar dar a lardin Suwayda da ke kudu maso yammacin kasar Siriya, inda dakarun gwamnati ke ci gaba da rufe hanyoyin da ke shiga lardin tun da safiyar Asabar, bayan kazamin fadan da aka gwabza tsakanin ‘yan kabilar Bedouin da mayakan Duruz a cikin birnin.
Hukumomin rikon kwaryar Siriya sun samu nasarar kwace iko da lardin, tare da kafa shingaye na kasa domin raba bangarorin da ke fada da juna bayan rattaba hannu kan yarjejeniyar tsagaita bude wuta. Sun kuma hana wucewar daidaikun mutane da ayarin motocin sojoji a kusa da lardin.