Kwamitin Tsaron MDD Ya Fara Tattaunawa kan Matsalolin Yankin Gaza

Kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya ya fara tattauna masifar da ta faru a Gaza tare da jaddada kawo karshen kisan kiyashi  yanki Kwamitin tsaron Majalisar

Kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya ya fara tattauna masifar da ta faru a Gaza tare da jaddada kawo karshen kisan kiyashi  yanki

Kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya ya gudanar da wani sabon zama domin tattauna batutuwan da suke faruwa a Gaza da kuma tabarbarewar al’amuran jin kai a yankin, inda ake ci gaba da yin kiraye-kirayen gaggauwa da kuma kira ga kasashen duniya da su dauki kwararan matakai na kawo karshen bala’in da ya biyo bayan yakin kisan kare dangi a yankin.

Majalisar Dinkin Duniya ta yi kira da a hanzarta dakatar da tilastawa al’ummar Gaza gudun hijira kamar yadda ta bukaci gwamnatin mamayar Isra’ila da ta ba da damar kai agajin jin kai ga al’ummar Zirin Gaza.

Mataimakin babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya mai kula da yankin Gabas, Mohamed Khaled Khari, ya tabbatar da cewa an kashe Falasdinawa kusan 300 a kusa da wuraren raba kayan agaji tun bayan jawabinsa na karshe a watan jiya.

“Mummunan halin da ake ciki a Gaza yana kara tabarbarewa tare da karuwar hasarar rayuka. Dole ne a daina yakin Gaza kuma a sako mutanen da aka yi garkuwa da su. Ayyukan da gwamnatin mamayar Isra’ila ke yi a Deir al-Balah ya haifar da karuwar ‘yan gudun hijira.”

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted