Iran Ta Zargi Amurka Da Isra’ila Da Keta DokokiDa Yarjeniyoyin Kasa Da Kasa

Wani babban Jami’in diblomasiyyar kasar Iran ya zargi Amurka da kuam HKI da laifin Zagon kasa ga dokokin kasa da kasa da kuma sabawa yarjeniyoyi

Wani babban Jami’in diblomasiyyar kasar Iran ya zargi Amurka da kuam HKI da laifin Zagon kasa ga dokokin kasa da kasa da kuma sabawa yarjeniyoyi da dokokin MDD.

Kazen Gharibabadi mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran kan al-amuran sharia na kasa da kasa yana fadar haka a jiya Laraba a majalisar dinkin duniya a birnin NewYork na kasar Amurka, a lokacinda yake jawabi a gaban kwamitin tsaro na MDD dangane da kasar Falasdinu.  

Gharibabadi ya bayyana cewa, Amurka da HKI sune manya-manyan masu haddasa rashin tsaro a kasashen yankin Asiya ta yamma.

Jami’in diblomasiyyar ya bayyana cewa Amurka da HKI ne suke haddasa halin da ake ciki a Gaza, na yuwan da kuma kisan kiyashi a Gaza da kashesu hanyar daukar yunwa a matsayin makami. Hakama tashe-tashen hankula a kasashen Yemen, Siriya da kuam Lebanon.

Banda haka wadanan kasashen biyu ne suka haddasa yakin kwanaki 12 a kan kasar Iran a cikin watan Yunin da ya gabata.

Yace wadan nan kasashe ne suke haddasa matsaloli da ruda gidajen falasdinawa a yankin yamma da kogin Jordan, Yace HKI ta kori miliyoyin Falasdinawa daga gidajensu ta maidasu yan gudun hijira a kasashe makobta da kuma da sauran kasashen duniya,

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments