Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya bayyana cewa: Sojojin mamayar Isra’ila sun kashe kananan yara 45 a Zirin Gaza a cikin kwanaki biyun da suka gabata, kuma wani abin tunatarwa shi ne cewa: Yara a Gaza na shan wahala da farko, suna fama da yunwa kowace rana kuma suna fuskantar hare-haren wuce gona da iri da muggan makamai kan mai uwa da wabi.”
A cikin wata sanarwa da Asusun ya fitar a ranar Juma’a, ya jaddada yi kira da a kawo karshen wahalhalu da kashe-kashen yara a kullum.
A nata bangare, Hukumar Lafiya ta Duniya ta bayyana cewa: “Hare-haren sojojin gwamnatin mamayar Isra’ila na ci gaba da yin mummunan tasiri ga cibiyoyin kiwon lafiya, ciki har da asibitin Turai na Gaza da ke Khan Yunis, wanda yanzu ya daina aiki.”