Rikici Tsakanin Faransa Da Aljeriya Ya Shiga Wani Sabon Salo Na Koran ‘Yan Kasashen Juna Daga Kasashensu

An samu bullar rikicin da ba a taba ganin irinsa ba a dangantaka tsakanin Aljeriya da Faransa Rikicin ma’aikatan harkokin diflomasiyya tsakanin Aljeriya da Faransa

An samu bullar rikicin da ba a taba ganin irinsa ba a dangantaka tsakanin Aljeriya da Faransa

Rikicin ma’aikatan harkokin diflomasiyya tsakanin Aljeriya da Faransa ya dawo kan gaba a fagen dakaddamar da ke tsakaninsu.

Rikici dai na kara kamari ne tsakanin Aljeriya da Faransa, tun daga rikicin korar ‘yan kasar Aljeriya daga Faransa zuwa rikicin korar ma’aikatan diflomasiyyar Faransa daga Aljeriya. Kasashen biyu sun tsaya a gaban nauyin tarihin mulkin mallaka ba tare da shawo kan shi ba. Aljeriya ta gayyaci mukaddashin jakadan Faransa domin sanar da shi aniyarta ta korar karin jami’an Faransa da ke aikin taimakon wucin gadi daga kasarta.

Wannan kiran ya biyo bayan maimaita cin zarafi mai tsanani da bangaren Faransa ya yi ne, yana wakiltar keta doka da aka kafa da kuma keta tsarin al’ada don nada ma’aikata a ofisoshin diflomasiyya da na ofishin jakadancin Faransa da aka amince da su a Aljeriya.

Akalla ma’aikatan Faransa 15 ne aka nada don gudanar da ayyukan diflomasiyya ko na ofishin jakadancin a kasar Aljeriya, ba tare da bin ka’idojin da suka dace ba, gami da sanarwa a hukumance ko kuma ba da izini, kamar yadda ka’idoji da yarjejeniyoyin kasa da kasa suka bukata.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments