Tsohon Fira ministan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila Ehud Barak ya yi kira da a hambarar da Benjamin Netanyahu da gwamnatinsa, yana mai zarginsa da yin sakaci wajen kubutar da fursunonin yahudawa da suke hannu ‘yan gwagwarmaya a Zirin Gaza.
Barak ya ce: Netanyahu yana sakaci da rayuwar fursunonin yahudawa da ake tsare da su a Gaza domin faranta wa masu tsattsauran ra’ayi a gwamnatinsa rai.” Ya bayyana shi a matsayin mai sakaci wajen gudanar da ayyukansa, da kuma ci gaba da kisan kiyashi a Zirin Gaza domin karecmanufofin siyasa saboda neman ci gaba da mulki.
A wata hira da yayi da tashar talabijin mai zaman kanta ta Isra’ila ta 12, Barak ya bayyana cewa: Netanyahu “yana sakaci da rayukan mutanen da ake tsare da su a Gaza domin farantawa masu tsatsauran ra’ayi a gwamnatinsa rai. Don haka ya jaddada yin kira ga ‘yan adawa da su dauki matakin ruguza gwamnatin Netanyahu maimakon ceto shi.