Wani babban jami’in kungiyar Hamas wacce take iko da Gaza ya bada sanarwan cewa an fara tattaunawa da HKI ta kawo karshen wannan yakin a birnin doha ba tare da shimfida wasu sharudda ba.
Shafin yanar gizo na labarai Arabnews ya nakalto Taher Annunu daga daga cikin manya-manyan jami’an kungiyar ta Hamas yana fadar haka. Ya kuma kara da cewa tattaunawar zata hada dukkan matsalolin da ke tsakanin bangarorin biyu. Annunu ya ce kungiyarsa zata gabatar da dukkan abubuwan da yakamata a tattaunawa a kansu kama daga tsagaita wuta, musayar fursinoni da kuma ficewar sojojin HKI daga Gaza.
Majiyar HKI ta nakalto firai ministan HKI Benyamin Natanyahu yana cewa ya aika tawagar tattaunawarsa zuwa birnin Doha na kasar Qatar.