Jagora: Jawaban Trump A Ziyar Da Ya Kai Wasu Kasashen Larabawa Na Yankin Tekun Farisa Abin Kunya Ne Gare Shi Ga Kuma Amurkawa

Jagoran juyin juya halin musulunci a nan Iran Imam Sayyid Aliyul Khaminae ya yi watsi da wasu kalaman shugaban kasar Amurka Donal Trump a ziyar

Jagoran juyin juya halin musulunci a nan Iran Imam Sayyid Aliyul Khaminae ya yi watsi da wasu kalaman shugaban kasar Amurka Donal Trump a ziyar da ya kammala a wasu kasashen larabawa na yankin Tekun farisa, ya kuma bayyana wasu kalamansa a matsayin kungiya ga kansa da kuma mutanen Amurka. Har’ila yau Jagoran ya kara da cewa da dama daga cikin maganganunsa basu cancanci maida martani ba.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Jagoran yana fadar haka a yau Asabar, a lokacinda yake ganawa da wasu malaman makaransu daga larduna daban daban na kasar, a Husainiyyar Imam Khonaini (q) a nan Tehran.

Jagoran ya kara da cewa : Trump yace yana son amfani da karfin da Amurka take da shi don samar da zaman lafiya wanda karaye ce, saboda. Shi da jami’an gwamnatin Amurka da suna amfani da karfi wajen kashe mutanen Gaza, sannan suna farwa kasashe da yaki, inda zasu iya. Haka ma suna amfani da karfi wajen goyon bayan ma’aikatansu a kasashen duniya da dama don kare bukatu da manufofinsu a wadannan kasashe.

A wani wuri a jawabinsa jagoran ya bayyana cewa, gaskiya ne ana amfani da karfi don samar da zaman lafiya a wani lokaci, kamar yadda JMI take bunkasa karfinta na makamai da kuma dabarbarun yaki a ko wani lokaci.

Amma Amurka da kawayenta da dama suna amfani da karfinsu suna goyon bayan HKI don ta kashe yara a Gaza, ta rusa asbitoci a gaza, ta kuma rusa gidajen mutane a Gaza da Lebanon da Yemen da duk inda zasu iya yin haka.

Imam Khaminae ya sifanta HKI a matsayin mabubbukan barna da rashin zaman lafiya da cusa  gaba cikin kasashen yammacin Asiya. Yace ” HKI a wannan yankin tana kamar cutar daje ce, wacce dole a tumbuketa daga wannan yankin.

Dangane da fadin shugaba Trump kan cewa gwamnatocin kasashen yankin ba zasu iya tabbata a kan kujerun shugabancin kasashensu na kwana goma ba. Jagoran yace wannan ma kariya ce ba haka ba, wannan tsarin ya fada, tare da gwagwarmayan kasashen wannan yankin sai an kori Amurka daga cikinsa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments