Matan Falasdinawa A Gaza Suna Fama Da Yunwa Mai  Tsanani Da Kuma Hare-haren HKI

Falasdinawa mazauna yankunan Khan-Yunus dake kudancin zirin Gaza suna fama da matsananciyar yunuwa, a lokaci daya suna fuskantar hare-hare masu tsanani daga sojojin HKI. Mata

Falasdinawa mazauna yankunan Khan-Yunus dake kudancin zirin Gaza suna fama da matsananciyar yunuwa, a lokaci daya suna fuskantar hare-hare masu tsanani daga sojojin HKI.

Mata mazauna yankin sun fi fuskantar matsaloli saboda kananan yaran da suke tare da su, alhali kuma an rushe gidajensu.

A tsawon yakin kisan kiyashin da HKI take yi, matan da su ka yi shahada sun kai 12,000 da 400. Bugu da kari wasu matan da sun kai 14 sun bace ba a gano su ba, sai kuma wasu matan masu ciki da sun kai 60,000 da suke fuskantar hatsari mai tsanani saboda rashin kula da su, da kuma rusa asibitoti da sojojin HKI su ka yi.

A cikin wani tanti a Khan-Yunus da akwai wata mace mai suna Ummu Muhamad da take rayuwa da ‘ya’yanta 7, bayan da maigidanta ya yi shahada sanadiyyar harin sojojin HKI.

Matar ta bayyana cewa, baya ga mijinta da akwai wani daga cikin ‘ya’yanta da ya yi shahada, kuma su da suke a raye suna da bukatuwa da magungunan da samunsu yake yin wahala saboda halin yaki da ake ciki.

Ta kuma bayyana cewa; Muna fama a yunuwa mai tsanani,babu wanda zai taimake mu, kuma fulawar da ake da ita, ta yin burodi ta kare.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted