Shugaban kasar Rasha Vladimir Puttin Ya gana da tokwaransa na kasar Masar Abdul alfattah Asisi bayan halattar bikin cika shekaru 80 da nasarar da kasar Rasah ta samu kan sojojin Nazi a yakin duniya na biyu wanda aka gudanar a birnin Mosco.
Shafin yanar gizo na labarai ya bayyana cewa harkokin kasuwanci a tsakanin kasashen biyu tana bunkasa inda a shekarar da ta gabata ya kai dalar Amurka biliyon $9.
Har’ila yau kowa ya san yadda kasar Masar ta zama sansanin sojojin kasar Rasha a lokacin yakin duniya na biyu. Da kuma yadda kasar ta taimakawa kasar Rasha a yakin da ta fafata da sojojin Nazi na kasar Jamus.
Har’ila yau shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya godewa shugaban kasar Brazil Lula de Silva a kan ziyarar da ya kawo kasar Rasha, ya kuma kara da cewa danganta tsakanin kasashen biyu yana kara karfi a hankali a hankalai.