Jakadan JMI a MDD ya musanta zargin kamfanin dillancin labaran reuters dangane da rotohonsa na cewa JMI tana aika makamai masu linzami zuwa kasar Rasah don taimakawa kasar Rasha yakin da take fafatwa da kasar Ukraine fiye da shekaru 3 da suka gabata.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto
Ofishin jakadancin JMI dake birnin NewYork ya kara da cewa, abin mamaki da kamfanin dilancin laraban reuters, shi ne ba wannan ne karo na farko yake yada labaran karya a duniya wanda wai yake samu daga wasu wadanda basa son a bayyana sunansu.
Kafin haka dai JMI ta sha nanata cewa bata bayan wani bangare daga cikin bangarori biyu da suke fafatawa a kasar Ukraine.
Don haka bata taba taimakawa kasar Rasha da makamai don yakar kasar Ukraine ba, kuma bata taba taimaka kasar Ukraine.
Ofishin jakadancin ya bayyana cewa ra’ayinta da so samu ne ta zama mai shiga tsakani don warware rikicin kasar ta Ukraine.
Amma reuters ya ci gaba da bada labaran karya wadanda suke cewa tana shirin aikawa kasar Rasha damdamalin cilla makamai masulinzami wadanda Iran ta aikawa kasar Rasa a Bara, kamar yadda Amurka take zargin hakan.