Manistan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya gana da tokwaransa na kasar Saudiya Faisal Bin Farhan a birnin Jeddah inda bangarorin biyu suka tattauna kan al-amuran da suka shafi yankin, musamman batun Falasdinawa da kuma halin da suke ciki musamman a yankin gaza.
Inda HKI take kashesu da yuwan, sannan tana ci gaba da rusa gidajensu a yankin yamma da kogin Jordan.
Har’ila yau, kasashen biyu a matsayin manya-manyan kasashen a yankin yammacin Asiya sun yi kokarin kyautata dangantaka a tsakaninsu. Kuma Aragchi ya je kasar ta saudiya ne don kyautata dangantaka tsakanin kasashen biyu da kuma zurgaga al-adu da al-amura da suka hada kasashen biyu daga ciki har da kasancewarsu kasashe musulmi.
A wani bangare Aragchi ya fadawa tokwaransa inda aka kwana dangane da tattaunawar da kasar take yi da kasar Amurka dangane da shirinta na makamashin Nukliya.