Sojojin  HKI Sun Rushe Gidajen Falasdinawa Fiye Da 100 A Yammacin Kogin Jordan

A cikin wata daya kadai sojojin HKI sun rushe gidajen Falasdinawa 152 a yammacin Kogin Jordan. Majiyar Falasdinawa ta ambaci cewa a kudancin garin Khalil

A cikin wata daya kadai sojojin HKI sun rushe gidajen Falasdinawa 152 a yammacin Kogin Jordan.

Majiyar Falasdinawa ta ambaci cewa a kudancin garin Khalil ‘yan mamayar sun rushe gidaje 25 da kuma wasu cibiyoyi, da hakan ya sa adadin gidajen da su ka rushe zuwa 152 kamar yadda hukumar Falasdinu ta ambata.

Bugu da kari, majiyar Falasdinawan ta ce, ‘yan mamayar sun kuma aike wa da wasu cibiyoyin da gidaje 46 gargadin cewa za su rushe su, da yin kira da  su fice daga cikinsu.

Wata cibiyar ta Falasdinawa ta ce fada wa kamfanin dillancin labarun “Anatoli’ cewa; ;yan mamayar sun rushe gidaje 96 da mutane suke rayuwa a cikinsu, sai kuma wasu gidaje 10 da babu mutane a ciki.Haka nan kuma rusau din ya shafi wasu cibiyoyin noma 34.

Mafi yawancin gidajen da aka rushe dai suna a yankin Tubas ne, Khalil sannan kuma da birnin Kudus.

Wani rahoto ya ambaci cewa; A cikin watan da ya gabata,’yan mamaya suna nazarin gina matsugunan ‘ya share wuri zauna 27 a cikin birnin Kudus.

A gefe daya, ‘yan share wuri zauna din sun kai hare-hare akan Falasdinawa har sau 1693 wanda ya fara a cikin watan Afrilu. Hare-haren kuwa sun hada lalata hanyoyi da tunbuke bishiyoyi, a kwace filayen Falasdinawa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments