Majalisar Dinkin Duniya Ta Ce Masifar Yunwa Ta Kara Yin Kamari A Yankin Zirin Gaza Na Falasdinu

Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewa: Gaza na gaf da afkawa cikin babbar masifa saboda zaluncin ‘yan mamayar Isra’ila A yayin da gwamnatin mamayar

Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewa: Gaza na gaf da afkawa cikin babbar masifa saboda zaluncin ‘yan mamayar Isra’ila

A yayin da gwamnatin mamayar Isra’ila ke ci gaba da killace Zirin Gaza sama da watanni biyu, abubuwan da ke faruwa a kowace rana, abubuwa ne da suke yadda bala’i ke shafar kowane gida, kowane titi, da kowane yaro, tare da cewa a kowace rana, ana kara gargadin cewa; Lokaci ya fara kurewa don ceton abin da za a iya cetowa.

Ofishin yada labarai na gwamnati a Gaza ya sabunta gargadi game da bala’in da ke tafe saboda ci gaba da rufe mashigar yankin da kuma tsaurara matakan hana shigowa da madarar jarirai, da abinci mai gina jiki, da kuma taimakon jin kai.

Hakan ya wurga yara sama da 70,000 cikin fuskantar matsalar Rashin abinci mai gina jiki, yayin da wasu yaran Falasdinawa ‘yan kasa da shekaru biyar 3,500 ke fuskantar barazanar yunwa. Kimanin yara 290,000 ne ke gab da mutuwa, yayin da fiye da yara miliyan daya ke fama da rashin isasshen abinci a kullum rana. Ofishin ya bayyana wannan lamari a matsayin kisan kiyashi da aka yi a cikin abin kunya da kasashen duniya suka yi shiru, inda ya yi kira da a dauki matakin gaggawa don kawar da wannan killacewar tare da kin ba da damar shigar da kayan agajin jin kai domin ceto rayukan yara.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments