Sojojin Sudan Da ‘Yan Tawayen Kasar Suna Ci Gaba Da Gwabza Fada A Wasu Saasan Kasar

Ana ci gaba da gwabza kazamin fada a yammacin Sudan tsakanin sojojin Sudan da dakarun kai daukin gaggawa na kasar Jiragen saman yaki marasa matuki

Ana ci gaba da gwabza kazamin fada a yammacin Sudan tsakanin sojojin Sudan da dakarun kai daukin gaggawa na kasar

Jiragen saman yaki marasa matuki ciki na dakarun kai daukin gaggawa sun kai hare-hare kan sansanin sojin sama na Osman Digna da ke gabashin Sudan, inda suka janyo bullar gobara a ma’ajiyar harsasai. Jiragen saman marasa matuka ciki dai sun kai hari kan filin jirgin na Kassala cikin kwanaki biyu. Yayin da a yammacin Sudan, sojojin Sudan sun yi ruwan bama-bamai a kan wani jirgin saman dakon kaya a filin jirgin sama na Nyala da ke yankin Darfur ta Kudu, wanda ke jigilar kayan aikin soji zuwa ga dakarun kai daukin gaggawa na Rapid Support Forces.

A yammacin Sudan na ci da wuta tare da hare-haren jiragen saman yaki marasa matuka ciki da kuma luguden harsasai, kuma sojojin sun janye daga yankin Nahud da ke yammacin Kordofan, kafin nan gaba su sake dawowa, kamar dai yadda suka yi a jihar Al-Jazirah da ke tsakiyar Sudan, a cewar wata majiyar soji.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments