Iran ta yi kakkausar suka da kakkausar murya kan zargin Amurka da da na Isra’ila suka cewa ta na da hannu a hare-haren ramuwar gayya na kasar Yemen.
Iran ta ce zarge zagren basu da tushe balle makama.
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araghchi ya fada a yammacin jiya Lahadi cewa, matakin da kasar Yemen ta dauka na goyon bayan al’ummar Falasdinu, wani mataki ne mai cin gashin kansa, wanda aka dauka a matsayin goyan bayan Palasdinawa.
Babban jami’in diflomasiyyar na Iran ya jaddada cewa, sojojin Amurka ne suka shiga yakin domin tallafawa kisan kiyashin da gwamnatin sahyoniyawa ke ci gaba da yi a zirin Gaza.
Don haka Araghchi ya soki Amurka da aikata laifukan yaki ta hanyar kai hare-hare kan ababen more rayuwa da wuraren fararen hula a garuruwan Yemen.
Araghchi ya kira hare-haren da Amurka ta kai kan kasar Yemen a matsayin cin zarafi ga kundin tsarin mulkin Majalisar Dinkin Duniya da muhimman ka’idojin dokokin kasa da kasa.
Babban jami’in diflomasiyyar na Iran ya ci gaba da cewa zargin da ake yi na baya-bayan nan wata dabara ce ta karkatar da hankali daga laifukan da gwamnatin sahyoniyawan ta ke aikatawa a Falastinu, da boye irin gazawar da Isra’ila da kawayenta suka yi a cikin dabarunta, da kuma tabbatar da ci gaba da tada zaune tsaye a yankin.