Sojojin Yemen sun sanar da killace sararin samaniyar Falasdinawa da yahudawan sahayoniyya suka mamaye
Sojojin Yemen sun sanar a yammacin jiya Lahadi cewa: Za su kakaba wa haramtacciyar kasar Isra’ila cikakken takunkumi ta sama, yayin da kamfanonin jiragen sama na kasa da kasa suka yi gargadin hadarin da ke tattare da zirga-zirga daga filayen jiragen saman yankunan Falasdinawa da aka mamaye. Wannan dai na zuwa ne a matsayin martani ga karuwar hare-haren da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ke kai wa a zirin Gaza.
Kakakin rundunar sojin Yemen, Birgediya Janar Yahya Sari’e, ya ce za su kakaba takunkumin ne ta hanyar kai hare-hare akai-akai kan filayen jiragen saman haramtacciyar kasar Isra’ila, musamman filin jirgin sama na Ben Gurion.
Sanarwar ta yi gargadi ga dukkan kamfanonin jiragen sama na kasa da kasa kan hadarin da ke tattare da hakan, inda ta yi kira gare su da su “soke dukkan tafiye-tafiyen jiragen da ke zuwa filayen jiragen sama na gwamnatin ‘yan mamaya masu tafka muggan laifuka domin kare lafiyar jiragensu da na kwastomominsu.”
Birgediya Janar Sari’e ya jaddada cewa: Kasar Yemen ba za ta amince da ci gaba da keta hurumin da makiya ke kokarin aiwatarwa ta hanyar kai wa kasashen larabawa irinsu Lebanon da Siriya hari ba, yana mai jaddada cewa “wannan al’ummar ba za ta ji tsoron bullar duk wani fada ba, kuma za ta ki mika wuya da rusuna wa azzalumai.”