Wani babban mai bawa jagoran juyin juya halin musulunci Imam Ayatullahi Sayyid Aliyul Khaminae shawara kan harkokin tsaro ya bayyana cewa hare-haren ‘WaaduSsadik na III’ don maida martani kan HKI saboda hare-haren da ta kaiwa Iran a shekarar da ta gabata suna kan hanya.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Manjo Janar Yahya Rahim Safavi yana fadar haka a jiya Jumma’a ya kuma kara da cewa, Tehran tana kan bakanta na maida martani kan HKI saboda hare-haren da ta kai kan wasu wurare a nan Iran daga cikin har da wani barikin sojoji a nan birnin Tehran a shekarar da ta gabata.
Safari ya kara da cewa, jinkirin da aka samu na maida-martani yana da hikima a cikinsa. Sannan karfin maida martanin sai ya nininka wadanta ta kai a wa’adussadik na II.
Ya kuma kara da cewa shugabanci a JMI yana da wayo, da dogon tunani da kuma tsari mai kyau.