Maduro Ya Bayyana Sakataren Harkokin Wajen Amurka Da Cewa Wawa Ne

Shugaban kasar Venezuela Nicolas Maduro ya bayyana sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio da yake ziyarar aiki a kasar Guyana da cewa, sakarai ne. A

Shugaban kasar Venezuela Nicolas Maduro ya bayyana sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio da yake ziyarar aiki a kasar Guyana da cewa, sakarai ne.

A yayin ziyarar da sakataren na  harkokin wajen Amurka ya kai zuwa kasar Guyana mai makwabtaka da Venezuela, ya ce, Amurka za ta mayar da martani mai karfi akan Venezuela idan har ta kai wa Guyanan hari.

Rubio ya kara da cewa; Idan haka ta faru, to kuwa Venezuela za ta gwammace kida da karatu a wannan rana.

Amurkan dai ta kulla yarjejeniyar tsaro da kasar ta Guyana a yayin ziyarar da Rubio ya kai.

Shi kuwa shugaban kasar ta Venezuela da yake mayar da martani ya ce; Marco Rubio wawa, ya zo yana yi wa kasar Venezuela barazana daga kasar Guyana, sannan ya kara da cewa; Venezuela ta fi karfin a yi mata barazana, domin ita kasa ce ta ‘yanci.”

Alaka a tsakanin Venezuela ta Amurka ta sake tabarbarewa tun bayan da shugaba Donald Trump ya hau karagar mulki, bayan da ya kara kakaba mata takunkumai, da kuma batun mayar da ‘yan hijirar kasar daga Amurka.

Share

4 1 vote
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments