Jaridar Ma’ariv ta Isra’ila ta bayyana adadin wadanda suka jikkata a cikin sojojin mamayar Isra’ila da kuma miliyoyin yahudawan sahayoniyya da suka samu matsalar tabin hankali a lokacin yakin Gaza
Jaridar “Ma’ariv” ta haramtacciyar kasar Isra’ila ta bayyana a jiya litinin, adadin wadanda suka mutu a cikin jerin sojojin mamayar Isra’ila a yayin mummunan ayyukan ta’addancin da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta kaddamar kan Zirin Gaza, wanda ya shafe tsawon watanni 15 kafin cimma yarjejeniyar tsagaita wuta da musayar fursunoni a watan Janairun da ya gabata.
A cewar jaridar, sojoji 15,000 da ke cikin sojojin mamayar Isra’ila suka jikkata tun farkon yakin ranar 7 ga watan Oktoban shekara ta 2023, yayin da wasu 846 suka sheka lahira.
Daga cikin wadanda suka samu raunuka, sojoji 8,600 ne suka sami raunuka daban-daban na jiki, yayin da wasu 7,500 suka samu matsalolin tabin kwakwalluwa ciki har da firgita, damuwa, tashin hankali, rikirkicewar tunani, kamar yadda jaridar ta nakalto daga sashin kula da dabi’ar ma’aikata da ke karkashin Ma’aikatar yakin haramtacciyar kasar Isra’ila.
Kanun labarai