Jagoran juyin juya halin Musulunci ya jaddada cewa: Barazanar makiya a kan kasar Iran da al’ummarta ba ta yi nasara ba
Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya bayyana cewa: Gagarumar zanga-zamga da al’ummar Iran suka gudanar a ranar 22 ga watan Bahman ta tabbatar da cewa barazanar makiya a kan Iran da al’ummarta ba ta cimma nasara ko yin tasiri ba.
Jagoran juyin juya halin Musuluncin yayin da yake karbar bakwancin dubban mutane daga lardin gabashin Azarbaijan a Husainiyar Imam Khumaini da ke Tehran fadar mulkin kasar a ranar Litinin din da ta gabata, a daidai lokacin da ake gudanar da bukukuwan zagayowar bore mai tarihi na al’ummar Tabriz a ranar 29 ga watan Bahman shekara ta 1356 wanda ya zo daidai da (18 ga watan Fabrairu shekara ta 1978), ya bayyana cewa: Tsare-tsaren barazana ta hanyar wasa da ra’ayin al’umma da watsa sabani kan neman haifar da shakku dangane da kotunan juyin juya halin Musulunci da kuma yada kokwanto game da iya kalubalantar makiya.
Jagoran ya kara da cewa: A wannan taro da ya samu halartar shugaban kasar Masoud Pezeshkian suna jaddada cewa: Makiya suna kokarin tarwatsa al’umma ta hanyar yaudara amma da yardan Allah har yanzu ba su samu nasara ba, kamar yadda suke kokarin girgiza zukatan al’ummar Iran da neman hana matasa samun karfin gwiwar himma da hubbasa a fagen kara ci gaban kasarsu.