Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Arazgchi ya kara jadda cewa JMI ba zata zauna a teburin tattaunawa da kasar Amurka ba a karkashin takunkuman tattalin arziki ba. Ya kuma kara da cewa Amurka ba zata iya tursasawa kasar Iran zama da ita ba.
Ministan ya kara da cewa, ba zakin baki mukeso ba, sai mun gani a kasa a sanya hannu a dakardu sannan mu gani a kasa.
Ministan ya fadawa tashar talabijin ta Al-Alam mai watsa shirye shiryenta da harshen larabcin a nan Tehran, ta kuma bayyana cewa, Trump ya bayyana cewa ya na bukatar tattaunawa da kasar Iran kan shirinta na makamashin nukliya tun watan farkon waten Fabrairu amma ba abinda muka gani a kasa.