Wasu daga cikin mutanen kasar Afirka ta kudu da suke dauke da cutar HIV suna yin koken cewa janye tallafin da Amurka ta yi a karkashin hukumar nan ta USAID, zai jefa rayuwarsu a tsakanin mutuwa da rayuwa.
Da akwai miliyoyin mutane a kasar ta Afirka Ta Kudu da suke dauke da cutar HIV da su ka cutu daga dakatar da ayyukan hukumar USAID akan kiwon lafiya.
Yankin KwaZulu-Natal dake kasar Afirka ta kudu, yana da masu fama da cutar ta HIV da sun kai miliyan 1.9 a bisa kididdigar 2022. A fadin kasar kuwa da akwai masu dauke da wannan cutar da sun haura miliyan 7.5 da shi ne adadi mafi girma a duniya.