Ministan watsa labarai na kasar Lebanon Mr Paul Marcos ya bada sanarwan cewa sojojin HKI sun fara janyewa daga yankunan da suke mamaye da su a kudancin kasar Lebanon. Wanda kuma zai bada daman ga sojojin kasar su maye gurbinsu.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto ministan yana cewa wannan sauyin zai kyautata al-amuran tsaro a yankin. Wanda kuma zai tabbatar da ikon kasar Lebanon a kan dukkan kasar ta.
Kafin haka dai majalisar dokokin kasar Lebanon ta bokaci ficewar dukkan sojojin kasashen waje daga kasar. Sannan bisa kudurin mai lamba 1701 na MDD rundunar UNIFIL zata taimaka wa sojojin kasar tabbatar da zaman lafiya a kan iyakokin HKI da kuma kasar Lebanon.
Labarin ya kara da cewa an ga sojojin Lebanon suna shiga yankunan da sojojin HKI suke ficewa a safiyar yau.
Sojojin lebanon sun shiga Maroun El Ras, Mahbib, Meiss Jabal, Blida, Houla da kuma Markaba.