Search
Close this search box.

Iran: Shirun Da Kungiyoyi Da Kasashen Duniya Suka Yi Duk Tare Da Kissan Kiyashi A Gaza Abin Kunya Ne

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Naseer Kan’ani ya bayyana cewa rashin tabuka kome wanda kungiyoyin kasa da kasa suka yi, da kuma kasashen musulmi

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Naseer Kan’ani ya bayyana cewa rashin tabuka kome wanda kungiyoyin kasa da kasa suka yi, da kuma kasashen musulmi da Larabawa suka yi su ne suka jawo mutuwar Falasdinawa fiye da dubu 40 a gaza, a yayinda Amurka da sauran kasashen yamma a fili suna bayyana goyon bayansu ga HKI a kissan kiyashin da take yi a Gaza.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Naseer Kan’ani kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran yana fadar haka a shafinsa na X.

Ya kuma kara da cewa ya zuwa yanzu yara kanana kimani 15,000 ne sojojin yahudawan suka kashe, sannan wasu mutane 10,000 kuma suna karkashin da gine-ginen da aka rusa.

Sai zuwa yaushe, kasashen duniya da kuma kungiyoyin kasa da kasa zasu ci gaba da yin shiru kan wannan ta’asar da HKI take aikatawa a Gaza? Kan’ani ya yi tambaya.

Kakain ma’aikatar harkokin wajen na Iran  ya kammala da cewa, idan al-amarin nan ya ci gaba a haka, wadannan kasashe da kuma kungiyoyi sun ji kunya a tarihin bil’adama a duniya. Kuma ba za’a taba yafe masu ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments