Kungiyar gwagwarmayar Falastinawa ta Hamas ta yi tsokaci kan kalaman mai shigar da kara na kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ICC, Karim Khan, kan kiran da ya yi na a kama tare da tsare Firaministan gwamnatin yahudawan Sahyudawa Benjamin Netanyahu, da kuma ministan yaki Yoav Galant, bayan shudewar watanni 7 suna aikata kisan kare dangi a Gaza.
A cikin wata sanarwa da ta fitar, Hamas ta yi kira ga mai shigar da kara na kotun ICC, da ya ba da umarnin kamawa da tsare dukkan masu aikata laifukan yaki, ciki har da dukkanin shugabannin gwamnatin mamaya ta yahudawan Isra’ila.
Kungiyar ta yi kakkausar suka kan yunkurin mai gabatar da kara na kotun na “daidaita azzalumai da kuma wadanda aka zalunta a matsayi daya” ta hanyar bayar da sammacin kama wasu shugabannin gwagwarmayar Falastinawa, inda suka bukaci a soke duk wani sammacin kama shugabannin gwagwarmayar Falasdinu saboda yin hakan ya saba ka’idojin Majalisar Dinkin Duniya da kudurorinta.
Shafin intanet na Amurka “Axios” ya bayyana cewa, matakin da mai shigar da kara na kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ya dauka zai haifar da karuwar mayar da Isra’ila saniyar ware a duniya, da kuma kara matsin lamba kan gwamnatin shugaban Amurka Joe Biden, na ya matsa lamba kan Netanyahu, domin kawo karshen yakin da yake yi kan al’ummar Gaza.
A ranar litinin mai shigar da kara na kotun ICC ya bukaci a ba da sammacin kama Netanyahu da Gallant tare da shugabannin kungiyar Hamas.
Yayin da yake ishara da Netanyahu da Gallant, babban mai shigar da kara ya jaddada cewa “lafukan cin zarafin bil’adama na daga cikin korafe-korafen da aka gabatar a matsayin wani bangare na kai hari kan fararen hula Falasdinawa, wanda kuma har yanzu suke ci gaba da aikatawa.”
Kafin wannan lokacin dai ‘yan majalisar wakilai daga jam’iyyun Democrats da Republican, sun gargadi kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa da cewa, idan hart a bayar da sammacin kame jami’an Isra’ila a kan yakin da suke yi kan al’ummar Gaza, to su ma za su dauki matakin mayar da martani a kan kotun ta ICC.