Yakin Gaza ya cika kwanaki 218 cur yayin da ake ci gaba da samun karin shahidai sakamakon hare-haren bama-bamai kan yankin
Hare-haren wuce gona da irin yahudawan sahayoniyya kan Zirin Gaza suna ci gaba da gudana, inda suka ciki kwanaki 218 a jere, a daidai lokacin da ake ci gaba da samun shahidai da jikkatan Falasdina sakamakon munanan hare-haren bama-bamai a kowace rana, yayin da kungiyoyin ‘yan gwagwarmayar Falasdinawa suka sanar da kai farmaki kan ayarin sojojin mamayar yahudawan sahayoniyya a yankuna da dama na Zirin Gaza.
A cikin kididdigar baya-bayan nan da Ma’aikatar Lafiya ta Falasdinu ta gudanar da bayyana cewa: Adadin wadanda suka yi shahada sakamakon hare-haren wuce gona da irin sojojin yahudawan sahayoniyya tun daga ranar 7 ga watan Oktoban bara zuwa yau, ya kai shahidai 34,943 da kuma jikkatan wasu 78,572 na daban.