Babban zauren Majalisar Dinkin Duniya ya yi kira ga Kwamitin Sulhu na Majalisar da ya tabbatar da ‘yancin Falasdinawa ta hanyar amincewa da kasar a matsayin mamba a majalisar.
Kudirin da UAE ta gabatar ya samu amincewar kasashe 143, yayin da 25 suka ce ba ruwan su, sai guda 9 da suka ki amincewa, da suka kada kuri’ar kin amincewa da suka hada da : Amurka, Isra’ila, Argentina, Jamhuriyar Czech da Hungary.
Daftarin ya fayyace cewa Falasdinu ta cika sharuddan da ake bukata don zama memba,” kuma “don haka ya kamata a shigar da ita cikin Kungiyar.”
Masana na ganin wannan babban sako ne da aka aika wa kwamitin sulhu da Amurka.
Amurka dai, wacce ke adawa da duk wani amincewa da wani abu kamar haka, ba tare da cimma yarjejeniya da tsakanin kawarta Isra’ila da Falasdinawa, ta yi gargadin a wannan Juma’a, cewa idan batun ya koma ga Majalisar, tana tsammanin daukar mataki irin na watan Afrilu”.
Kwamitin Tsaro na Majalisar ta Dinkin Duniya ne kawai yake da damar tabbatar da hakan.
Zaben na ranar Juma’a ya nuna irin goyon bayan da ake nuna wa kasar Falasdinawa.
Falasdinu dai na da matsayin kasa ‘yar sa ido tun shekarar 2012.