Kasashen Larabawa sun yi maraba da kudurin babban zauren Majalisar Dinkin Duniya kan batun neman sanya Falasdinu a matsayar cikakkiyar mamba a Majalisar Dinkin Duniya
Matsayin babban zauren Majalisar Dinkin Duniya na amincewa da kudurin da ke goyon bayan bukatar kasancewar Falasdinu a matsayin cikakkiyar mamba a Majalisar Dinkin Duniya ya samu karbuwa daga kasashen Larabawa masu yawa, inda suka bayyana shi a matsayin “kudiri mai tarihi.” Yayin da yahudawan sahayoniyya suka gwada tsananin bacin ransu kan matsayin babban zauren.
A safiyar jiya Juma’a ne zaman taron babban zauren Majalisar Dinkin Duniya ya amince da wani kuduri da kungiyar kasashen Larabawa da wasu kasashe suka gabatar, inda suke tabbatar da cewa Falasdinu ta cancanci zama cikakkiyar mamba a Majalisar Dinkin Duniya, kamar yadda doka ta 4 ta Yarjejeniyar Majalisar Dinkin Duniya ta tanada, don haka ya dace a karbe ta a matsayin cikakkiyar memba a Majalisar.
Kasashe 143 ne suka kada kuri’ar amincewa da kudurin, yayin da wasu 9 suka nuna adawa da shi, wasu kasashe 25 kuma suka kaurace wa kada kuri’a, a cewar shafin yanar gizon Majalisar Dinkin Duniya.