Search
Close this search box.

Iran: Jami’an Tsaro Na Kan Iyaka Wadanda Aka Kaiwa Hari A Sistan Buluchistam Sun Yi Shahada

Iran: Jami’an Tsaro Na Kan Iyaka Wadanda Aka Kaiwa Hari A Sistan Buluchistam Sun Yi Shahada

Jami’an tsaron kan iyaka wadanda aka kaiwa hare haren ta’adanci a wurare biyu a kudancin Sistan Buluchistan sun kai shahada.

Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya bayyana cewa, yansanda 2, da kuma jami’an sojoji 2 da kuma sojan sha kai wato (basij) guda  ne suka yi shahada bayana raunuka da suka ji a hannun yan ta’adda a garin chabahar lardin sistan buluchistan a daren Laraba.

Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya bayyana cewa an kashe mutanen 5 daga cikin yan ta’adda a musayar wuta fa su a lokacinda suka farwa jami’an tsaron.

Mataimakin ministan cikin gida kan al-amuran tsaron ciki gida ya bayyana cewa an shiga fafatawa da yan ta’addan ne a wurare uku a cikin lardin, kuma suna hada da Chabahar, Rosk da kuma Sarboz.

An sami cikekken nasar kan yan ta’adda a Rosk amma suna rika da wani dan gari a matsayin garkuwa, a kofar ragon da jami’an tsaro suka yi masu. Don haka jami’an tsaro wadanda abinda ya shafa suna aiki don ganin sun kubutar da wanda aka yiwa garkuwa da shi.

Sayyid Majid Mir-Ahamadi ya yi karin bayani a safiyar yau Alhamis inda yake cewa yanta’addan da suka kai hari kan dakarun Sepah a Chabahar suma basu sami nasara ba, amma kuma 4 daga cikinsu sun buye a cikin wani gini kusa da wurin, don haka suma kamar sun shiga hannu ne kawai. 

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Inline Feedbacks
View all comments