Search
Close this search box.

Iran: Jagora Ya Bukaci A Kawo Tunanin Mutane Da Dukiyoyinsu Cikin Manufar Tabbatar ‘Shi’arin’ Wannan Shekarar

Jagoran juyin juya halin musulunci a nan Iran Imam Ayatullahi Sayyid Aliyul Khamina’e ya bukaci gwamnatin shugabab Ra’isi ta sanmar da wani kwamiti wanda zai

Jagoran juyin juya halin musulunci a nan Iran Imam Ayatullahi Sayyid Aliyul Khamina’e ya bukaci gwamnatin shugabab Ra’isi ta sanmar da wani kwamiti wanda zai yi aiki a cikin kasa, don jawo hankalin mutane su zuba dukiyoyinsu don bunkasa tattalin arzikin kasar.

Kamfanin dillancin labaran IRNA ya nakalto Jagoran yana fadar haka a lokacinda yake jawabi a gaban jami’an gwamnati da sashen gudanarwa da shariar kasar a gidansa dake nan Tehran a jiya Laraba. Ya kuma kara da cewa manufa ita ce dukkan mutanen kasar su taimaka wajen cimma manufofin wannan shekara na bunkasa tattalin arziki tare da amfani da mutane ko tarayyar da su a wannan ci gaban.

Da ya juya kan ranar Kudu ta duniya mai zuwa kuma Imam Khaminae ya bukaci a gudanar da jerin gwanon Kudus na bana a cikin yanayi na musamman don irin halin da ake ciki a yankin da kuma gaza.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Inline Feedbacks
View all comments