Kasashen Tajikistan da Kazhaskistan sun shiga cikin jerin masu yin tir da harin sojojin HKI akan karamin ofishin jakadancin Iran a Syria.
A wani bayani da ma’aitakar harkokin wajen Tajikistan ta fitar ta yi Allawadai da harin na HKI akan karamin ofishin jakadancin Iran ,tare da bayyana shi a matsayin wanda yake cin karo da dokokin kasa da kasa,wanda kuma ba za a amince da shi ba.
Ita ma kasar Khazakhistan ta fitar da bayani daga ma’aikatar harkokin wajenta, tare da bayyana shi a matsayin wuce gona da iri da za a lamunta ba.
A ranar litinin da ta gabata ce jiragen yakin HKI suka kai hare hare kan karamin ofishin jakadancin kasar Iran da ke birnin Damascus babban birnin kasar Siriya inda Janar Zahidi da Janar rahimi na dakarun kare juyin juya halin musulunci a nan kasar Iran wato IRGC da wasu mutane 5 tare da su suka yi shahada.