Iran: Jakadiyar Kasar Bolivia Ta Taya Iran Juyayin Wadanda Hare Hare Kan Ofishin Jakadancinta A Siriya Suka Kai Ga Shahada

Jakadiyar kasar Bolivia a nan Tehran ta yiwa JMI jajen hare haren ta’addancin da HKI ta kai kan karamin ofishin jakadancin kasar a birnin Damascus

Jakadiyar kasar Bolivia a nan Tehran ta yiwa JMI jajen hare haren ta’addancin da HKI ta kai kan karamin ofishin jakadancin kasar a birnin Damascus na kasar Siriya.

Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto Romino Parasromus jakadiyar kasar Bolivia a Tehran tana fadar haka a jiya Laraba  Ta kuma kara da cewa, a madadin shugaban kasar Bolivia da kuma sauran kasashen Laten Amurka wadanda suka hada da Brazil, Cuba, Mexico, Nicaragua, Venezuela da kuma Uruguay suka mika ta’aziyyarsu ga ministan harkokin wajen kasar Iran da kuma dangin wadanda suka rasa rayukansu a hare haren da HKI ta kai kan karamin ofishin jakadancin JMI a kasar kasar Siriya.

Ta kuma kara da cewa hare haren sun sabawa dukkan dokokin kasa da kasa wadanda suka shafi diblomasiya da kuma mutunta hurumin ko wace kasa daga cikin kasashen duniya. Don haka sun yi tir da wannan harin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments