Gwamnatin Najeriya ta musanta zargin cewa tana da hannu a hare-haren da ake zargin ‘yan ta’adda ta kungiyar Lakurawa suka kai kan bututun man fetur wanda ya taso daga jumhuriyar Nijer zuwa kasar Benin a garin Gaya na jihar Doso a Jumhuriyar Najer.
Jaridar Premium times ta Najeriya ta nakalto ma’aikatar harkokin wajen kasar a Abuja na fadar haka a jiya Asabar. Ta kuma mika alhininta ga awkuwar hakan ga Jumhuriyar Nijer, sannan ta musanta zargin cewa tana taimakawa wadannan yan ta’addan.
Sanarwan ta kara da cewa gwamnatin Najeriya ta na yaki da yan ta’adda ta kungiyar Lakurawa don haka ba yadda zai yu ta taimaka mata, ko kuma wani daga cikin jami’an tsaron kasar su taimaka mata don aikata ayyukan ta’addanci a wata kasa.
A wani bayanin ma’aikatar harkokin waje ta Najeriya ta bayyana cewa, gwamnatin kasar ba ta da anniyar shigo da sojojin faransa kasar. Ta kuma bukaci mutanen kasar su yi wasti da dukkan labarai da suke nuna hakan.