Dubban mutane a Ghana sun gudanar zanga-zangar nuna adawa da nuna banbanci a yakin da gwamnatin shugaba John Dramani Mahamat ke yi da cin hanci da rashawa.
Masu zanga-zangar da jam’iyyar adawa ta NPP ke jagoranta sun bukaci hukumomin kasar su tabbatar da cewa ana binciken duk wadanda ake zargi da almundahana ba tare da la’akari da matsayinsu ko jam’iyyarsu ba.
Masu shirya zanga-zangar sun kuma bukaci a kara bayyana yadda ake gudanar da bincike da gurfanar da wadanda ake zargi da karkatar da kudaden jama’a. Gwamnatin Ghana ta ɗade tana cewa yaki da cin hanci na bukatar hukumomi su bi doka ba tare da nuna wa kowane bangare fifiko ba.
Jam’iyyar NPP, karkashin jagorancin Shugaban ‘Yan Adawa a Majalisa Alexander Afenyo-Markin, na ganin cewa akwai banbanci da nuna son rai a yaki da cin hanci da rashawa da gwamnati ke yi, kuma an tsara shi ne domin rarraba kan ‘yan adawa.