Ƙungiyar Ansaru mai alaka da Al-Qaeda ta ɗauki alhakin kashe fitaccen mai da’awar Qur’ani zalla, Yahaya Ibrahim Masussuka, a garin Dutsin-Ma da ke jihar Katsina. Ƙungiyar ta bayyana hakan ne a cikin wani sakon murya da ta fitar a yau Talata, 27 ga Oktoba, 2026, inda ta zargi malamin da kasancewa wanda ba ya bin Musulunci yadda ya kamata.
A cewar rahoton, mai magana a cikin saƙon muryar ya ce an kai harin ne da misalin ƙarfe 8:30 na dare. Sai dai rahotannin farko daga ƴansanda sun nuna cewa an kashe malamin ne a ranar Litinin, 26 ga Oktoba, da misalin ƙarfe 7:30 na yamma, a gaban gidansa da ke Dutsin-Ma.
An kashe shaikh Masussuka tare da abokinsa, Adamu Abubakar, lokacin da wasu mutane biyu da ke kan babur suka buɗe musu wuta. Ƴansandan jihar Katsina sun tabbatar da kisan, inda kwamishinan ƴansanda, Ali Umar Fage, ya bayar da umarnin tura jami’an tsaro domin bin diddigin wadanda suka aikata laifin. Ya zuwa lokacin fitar da rahotannin, ba a sanar da kama wani da ake zargi ba