Tare da cewa giwaye suna cikin dabbobin da masu yawon bude ido suke son gani, said ai gwamantin kasar Zimbabwe ta yanke hukunci yanka 50 daga cikinsu domin rabawa mutanen karkara namansu.
Wannan matakin na gwamnatin Zimbabwe ya zo ne saboda yadda giwayen suke kara yawa sosai a cikin shekarun bayannan. Haka nan kuma wuraren da ake killace su, sun yi kadan.
Majiyar dake kula da gandun dajin kasar ta ce; adadin giwayen ya rubanya har sau uku, wannan ne ya sa mahukuntar kasar su ka yanke shawarar yanka 50 daga cikinsu saboda a rabawa mutanen karkara.
A baya gwamnatin na Zimbabwe ya yi kokarin warware matsalar karuwar dabbobin ta hanyar ( GPS). Haka nan kuma tana amfani da wannan fasahar wajen gargadin mutanen Karkare idan wata dabba ta karaci kauyukansu.
A shekarar da ta gabata kasar ta Zimbawe ta kashe giwaye 200 saboda farin da aka fuskanta wanda ya sa aka sami karancin abinci a kasar.
A wanann shekarar dai adadin giwayen da za a yanka ba su wuce 50 ba, zuwa yanzu.