Zaftarewar Kasa Ta Kashe Al’ummar Kauye Gaba Daya Sai Mutum Guda Da Ya Tsira

Sama da mutane dubu ne suka mutu sakamakon zaftarewar kasa a yankin Darfur na kasar Sudan Sama da mutane 1,000 ne suka mutu sakamakon zaftarewar

Sama da mutane dubu ne suka mutu sakamakon zaftarewar kasa a yankin Darfur na kasar Sudan

Sama da mutane 1,000 ne suka mutu sakamakon zaftarewar kasa da ta hallaka daukacin wani kauye a yankin Darfur na yammacin Sudan, a wani lamari da aka bayyana a matsayin daya daga cikin bala’o’i mafi muni da aka taba fuskanta a tarihin Sudan a wannan zamani, a cewar kungiyar fafatukar ‘yantar da al’ummar Sudan (SLM) da ke iko da yankin.

Kungiyar a cikin wata sanarwa da ta fitar ta ce, zabtarewar kasa gaba daya ta lalata kauyen Tarsin da ke gabashin Jebel Marra, kusa da yankin Soni, tare da kashe daukacin al’ummarta, wadanda aka kiyasta sama da maza da mata da yara sama da dubu daya. Mutum daya ne ya tsira, bisa ga bayanin farko.

Sanarwar ta bayyana cewa, bala’in ya afku ne a ranar Lahadi “sakamakon ruwan sama mai karfi da ya afku a makon da ya gabata na watan Agusta.”

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted