Iran ta ce za a gudanar da zagaye na gaba na tattaunawa da Amurka a ranar Lahadi mai zuwa a Muscat, babban birnin kasar Oman.
Kakakin ma’aikatar Esmail Baghai a wata sanarwa da ya fitar ya ce “An shirya zagaye na gaba na tattaunawa tsakanin Iran da Amurka a ranar Lahadi mai zuwa a birnin Muscat.”
Tun a watan Afrilu, Tehran da Washington ke gudanar da shawarwarin kan shirin nukiliyar Iran na zaman lafiya.
An yi shawarwari guda uku a tsakanin kasashen biyu a birnin Muscat, yayin da sauran biyun suka gudana a Rome, babban birnin kasar Italiya.
Tehran da Washington sun gudanar da wadannan zagaye biyar na shawarwarin a shiga tsakanin kasar Oman, kan batun maye gurbin yarjejeniyar nukiliyar 2015, wadda Amurka ta fice daga cikinta a shekarar 2018.
Sai dai shawarwarin na fuskantar cikas sakamakon bukatar da Amurka ta yi na cewa Iran ta daina tace sinadarin Uranium a matsayin wani bangare na sabuwar yarjejeniyar.
Iran dai ta jaddada cewa, ba za ta yi watsi da hakkinta na inganta sinadarin Uranium ba, wanda yarjejeniyar hana yaduwar makaman nukiliya (NPT) ta tanada.