Isra’ila za ta saki fursunonin Falasdinawa 183 yau Asabar, a madadin wasu mutanenta uku daga cikin wadanda kungiyar Hamas ke garkuwa da su a Gaza a wani bangare na aiwatar da yarjejeniyar tsagaita bude wuta a Gaza da suka cimma.
Kamar dai a makon da ya gabata, za a yi musaya ta biyar a wurare biyu a zirin Gaza a jere inji rahotanni.
A maimakon haka, Isra’ila za ta saki fursunonin Falasdinawa 183, ciki har da 18 da aka yanke wa hukuncin daurin rai da rai, ciki har da wasu fitattun mutane irin su Iyad Abu Shidam, wanda Isra’ila ta yankewa hukuncin daurin rai da rai a Beersheva a shekara ta 2004.
Bayanai sun ce kimanin 111 daga cikin wadannan fursunonin ‘yan Gaza ne da ake tsare da su tun ranar 7 ga watan Oktoba.
Wannan dai shi ne karo na biyar da ake gudanar da musayar irin wannan tun bayan da yarjejeniyar tsagaita bude wuta a zirin Gaza ta fara aiki a ranar 19 ga watan Janairu, bayan shafe watanni goma sha biyar ana yakin na Gaza.
Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu zai sa ido kan musayar tun daga Amurka, inda ya fara wata ziyara a ranar Litinin, kamar yadda ofishinsa ya bayyana.
Tun bayan fara tsagaita wutar, an sako wadanda ake garkuwa dasu 18 da da fursunonin falasdinawa 582.
Kashi na farko na yarjejeniyar, wanda zai dauki tsawon makonni shida, ya tanadi mikawa Isra’ila jimillar mutane 33 da aka yi garkuwa da su, ciki har da akalla takwas da suka mutu, a madadin Falasdinawa 1,900.