Za’a yi Garambawul Kan Dokar Amfani Da Shafukan Sada Zumunta A Kasar Nijer

Gwamnatin jamhuriyar  Nijar ta bayyana aniyarta ta yin garambawul ga dokar tsarin amfani da shafukan sada zumunta irin su Whatsapp da Facebook da dai sauransu

Gwamnatin jamhuriyar  Nijar ta bayyana aniyarta ta yin garambawul ga dokar tsarin amfani da shafukan sada zumunta irin su Whatsapp da Facebook da dai sauransu  a kasar.

Ministan sadarwa na kasar Nijer sidi Mohammad Raliyu shi ne ya bayyana hakan, yana me cewa duk wani zaure na Whattsapp ko Facebook da ya kunshi mutanen  50 zuwa 100 dole ne yayi rajista a wajen hukuma don ci gaba da aikinsa.

Ministan ya ce zaurukan whattsap da Facebook na zama hanyoyin kasuwanci da kuma yaƙar gwamnatoci,  wannan yasa za ta bullon da sabon shiri tare da  wasu ƙasashen Afirka domin sake duba dokar da ta bada damar aiki da shafukan sada zumunta a Kasashen,  domin dakile amfani da ita ta hanyar da bata dace ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments