Za’a Fara Taron Makon Hadin Kai Karo Na 39 A Tehran

Babban sakataren hukumar samar da hadin kai takanin mazhabobin musulunci hujjatul islam shahriyori ya sanar cewa a gobe litinin 8 ga watan satumba ne zaa

Babban sakataren hukumar samar da hadin kai takanin mazhabobin musulunci hujjatul islam shahriyori ya sanar cewa a gobe litinin 8 ga watan satumba ne zaa bude taron makon hadin kai na 39 a nan birnin Tehran inda zai samu halartar malamai sama a 80 da baki 210 da kuma masu rajin kare hakkin bil adama guda 2800 daga kasashen duniya daban daban.

Haka zalika hujjatul islam shahriyari ya kara da cewa taron zai gudana tsakanin 8-10 na watan satumba wanda yayi daidai da lokacin zagayowar ranar haihuwar manzon All.. tsira da aminci su tababta gareshi da Alayensa da aka sanyashi a matsayin makon hadin kai, yace hadin kai tsakanin addinai da kusanto da mazhabobi a yau ya zama wani batun ne na diplomasiya.

Har ila yau ya kara da cewa duk wanda ke zalunci kuma yake kwace hakkin yanci ko zama ga alummar falasinu cin zarafi ne babba garesu, wannan yasa dukkan bani adam ya daukaka muryarsa, sai yan gwagwarmayar da jamhuriyar  musulunci ta iran suka zo da wani tsari wanda yake sama da batun hadin kai wato makaranta kalubalantar zalunci.

Daga karshe ya bayyana cewa a karon farko hukumar ta zabi malam naseer kali sarli daya daga ckin malaman ahlul sunnaa matsayin matakimakin sugaban hukumar ta samar da hadin kai tsakanin musulmi.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted